1) Ƴan duniya ba sa yarda da Ubangijinmu, A ransu ba sa ɗauka ya zama sarkinsu, Amma fa wata rana zai komo duniyan nan, Gama mulkin duniya duka nasa ne. KORUS Za ya komo wata rana, i, wataƙila yau, Za ya komo daga Sama domin ya fyauce mu, Jama'arsa sai murna tare da shi su ke, Gama mulkin duniya duka nasa ne. 2) Mu, ranan nan sai daɗi mai yawa za mu ji; Ba sauran ƃacin zuciya, ba sauran zunubi, Sai murnar ganin Yesu, Yesu mai fansarmu, Domin mulkin duniya duka nasa ne. Korus 3) Ko yau ne ya ke zuwa, mu ba mu sani ba. Ya ce mu yi ta tsaro, mu riƙa jiransa. Mun sani yana zuwa, ba shakka ko kaɗan. Gama mulkin duniya duka nasa ne. KorusVuoi tu? A KA HRUAINAK AH ktyr ạlnạs btqwly mzmwr 134 - mrnm Хошбəхтдир Мəсиһə үрəкдəн ạ̉ntẓry̱ ạlrb yạnfsy̱ Ты Господь неба и земли Боз ба ту меоем, боз бо ту мешинем Ne Görkemlidir Tanrısal Sevgi! يا صاحب القلب
Song not available - connect to internet to try again?