1) A cikin farko Allah ya Halitta sama da ƙasa. Ta wurin ikon maganarsa Duniya da kome sun zama. KORUS Mai iko, Mai iko Allah ne Mai ikon kome, Mai iko, Mai iko Allah ne, Mai ikon dukan kome. 2) Ҡasa fa duka wofi ce Duhu ya rufe ruwaye. Rana ta fari Allah ya ce Bari haske shi kasance. Korus 3) Rana ta biyu Allah ya ce Bari sarari ya kasance, Kuma ya raba ruwaye Haka ya zama gaba dai. Korus 4) Rana ta uku tekuna Sun tattaru wari ɗaya. Ciyawa da itatuwa Kowane masu bada ƙwaya. Korus 5) Rana ta huɗu an gani Can cikin sama haskoki Bisa duniya su yi mulki Rana da wata da tamrari. Korus 6) Rana ta biyar Allah ya ce Kifi su cika ruwaye, Tsuntsayen sama su yalwaita, Su haifu har duniya ta cika. Korus 7) Rana ta shidda bisashe Ya yi su, masu-rarrafe Mutum da mananinsa ne Haka ya gam aikin ne. Korus 8) Rana ta bakwai Allah fa Ya huta daga aikinsa Haka mu kuma ƴayansa Mu huta rana guda kuwa. Korusاللي يجيلك ربي 奉献 كان قلبي اسود Він так взяв мене за руку Quién es como tú Миний хамгийн даруу сэтгэлд Ёр-ёр Кішкене бала أرجوك يا ابني تعال Hər tərəfi bürümüşdür qaranlıq
Song not available - connect to internet to try again?