1) A cikin farko Allahnmu Ya hallici dukan abu Cikin sama da akan duniya Dukan abin da kyau. 2) Ya hallici su mutane Su Adamu, da Hawa'u Ya sa su cikin gona ta Aidin Su aikace ta kuwa. 3) Ya dokace su Adamu Su Hawa'u kada su ci Daga icce na tsakar gona Ko mutuwa za su yi. 4) Shaiɗan ya shiga gonar nan Ya jarabci Hawa'u dai Ya sa ta shakkar maganar Allah Ta bi maganarsa. 5) Ta ɗiba ɗiyan iccen nan. Ashe, ta ci, ta ba miji Sun ɓoye daga murya ta Allah Sabo da tsoronsa. 6) Allah ya yi masu horo Ga maciji, la'ananne ne shi Mace ta haifa da baƙinciki Wahala tata ce. 7) Da zufa bisa fuskarka Ya Adamu, ka ci abincinka Ҡasa ta haifi ƙayayuwa kuma Zan kore ku da nan. 8) Allah ya kashe ɗan rago Da fatarsa ya rufe wofinsu Ya faɗa masu akwai Mai Zuwa Mai Ɗauken laifofi. 9) Mun gaji halin Adamu Duk mutane na duniya Amma ya aiko Yesu Mai Ceto Kama da ɗan rago. 10) An kashe Yesu Ɗan Allah Da jininsa ya kwashe laifina Yanzu na zama ta Allah kuma Ta wurin bangaskiya. 11) Na gode maka ya Allah Don ƙamnarka, don gafara Ka taimake ni, in bi ka kullum. Da zuciya ɗaya fa, Allahna.گاڤا مسيح كَتَه دْلِه مْن Мəсиһə үз тут сəн Сэнтийд залрагч - Их Усны шуугиан ยังมีสายธาร ạ̉yhạ ạlqdws Ще променим историята Ty jsi miloval spravedlnost Plášť svoj noc, keď prestiera Humble Yourself In The Sight Of The Lord tʿạlwạ ạ̹ly yạ jmyʿ
Song not available - connect to internet to try again?