1) A cikin ikonka, ya Yesu Kristi, Za mu tafi mu yi ta aikinka. Idan ka bi da mu, ya kai Mai Iko, Ba za mu ji tsoron duk duniya ba. Idan ka bi da mu, ya kai Mai Iko, Ba za mu ji tsoron duk duniya ba. 2) Sunanka, Yesu Kristi Almasihu, Sunanka dai duk mafi daɗi ne. Kai ne adalcinmu, kai ne Mai Ceto, Kai ne Sarkinmu, kai mai daraja. Kai ne adalcinmu, kai ne Mai Ceto, Kai ne Sarkinmu, kai mai daraja. 3) Gare ka mu ke dogara, ya Yesu, Inda ka nufa duka za mu bi, Ko cikin daɗi, ko a cikin wuya, Ko cikin mutuwa, mu dai nake ne. Ko cikin daɗi, ko a cikin wuya, Ko cikin mutuwa, mu dai naka ne. 4) A cikin ikonka, ya Yesu Kristi, Alherinka ya fi bukatarmu. Mu kuwa mun fi gaban masu nasara Don ƙaunarka, ya Ubangijinmu. Mu kuwa mun fi gaban masu nasara Don ƙaunarka, ya Ubangijinmu.Yüreğimdeki övgü Ты Создатель миров Oh Duniya Таң атқаннан Сені Più solo non sarò Şapte îngeri am văzut zburând Blessed be the Name روحي يا محبوسة Vengo, Jesús, A Ti ạḥmdk
Song not available - connect to internet to try again?