KORUS Aike da abincinka, a bisa ruwaye, Gama za ka same shi, bayan ƴan kwanaki. (2x) 1) Ga wasu bayi uku, aka yi kiransu, Ubangijinsu ya damƙa, masu dukiyarsa. Ga wani talent biyar, ga wani talent biyu, Ga wani talent ɗaya, gwalgwadon kowa. (Solo: "Ɗan'uwa.") Korus 2) Bawa mai talent biyar, da mai talent biyu, Suka fidda tsoro, suka yi bangaskiya. Suka jujjuya kuɗin, suka sami riɓa, Ubangijinsu ya sa, masu albarka. (Solo: "Ƴar'uwa") Korus 3) Bawa mai talent ɗaya, shi kuwa ya ji tsoro, Ya yi haƙi a ƙasa, ya ɓoye talent nan. Ubangijinsa ya ce, kai mugun bawa, Ku jefa cikin, baƙin duhu. (Solo: "Duka") Korus 4) Ƴan'uwa mu yi koyi, da mai talent biyar, Mu fidda tsoro, mu yi bangaskiya. Mu aike da abincinmu, a bisa ruwaye, Gama za mu same shi, bayan kwanaki. Korusبتفرحنـي ياربـي تمـلـي NI LE THLA AN LANH LIOAH Muna Zuwa Wurin Yesu Mai Ceto گولعوفادا قادالۇۇعا ىيسا باراتات Помоги понять 你遇见主了吗 hwdẖạ kmạ ạ̹n Иисус Ты моя радость Náš Otče svatý v nebesích Tac şi privesc ochii adânci
Song not available - connect to internet to try again?