1) Aka haife shi a Baitalahmi, Yesu Ɗan Allah ya zo duniya. Abin al'ajabi! Ƙauna ta sa Ya sauko domina. Ya sauko domina, ya sauko domina. Abin al'ajabi! Ƙauna ta sa Ya sauko domina. 2) Can bayan birni a kan giciye Yesu ya mutu, ya kuwa ba da rai, Abin al'ajabi! Ƙauna ta sa Ya mutu domina. Ya mutu domina, ya mutu domina. Abin al'ajabi! Ƙauna ta sa Ya mutu domina. 3) Dā, na yi nisa da Allah sosai, Can cikin jeji na ɓata sarai. Abin al'ajabi! Ƙauna ta sa Yesu ya cece ni. Yesu ya cece ni, Yesu ya cece ni. Abin al'ajabi! Ƙauna ta sa Yesu ya cece ni. 4) Yesu ya koma a wurin Uba Amma zai dawo a duniyan nan. Abin al'ajabi! Ƙauna ta sa Zai kai ni gidansa. Zai kai ni gidansa, zai kai ni gidansa. Abin al'ajabi! Ƙauna ta sa Zai kai ni gidansa.In Jesus Naam سْپاس أي خوَدا Торжествуй пред Ним مش كفاية Slož, co srdce tísní Всемогущий о Бог Святый Sei tu Bul Qudaı jaratty ǵoı aspan jerdi Жараткан жерди да Ježiš volá: Skoro už prídem
Song not available - connect to internet to try again?