1) Akwai haske yanzu cikin zuciyata Tun Yesu ya zo wurina. Aka gafarta mini duk zunubina Tun Yesu ya zo wurina. KORUS Tun Yesu ya zo wurina, Tun Yesu ya zo wurina, Ina da kwanciyar rai, Har da murna sosai, Tun Yesu ya zo wurina. 2) Yanzu dai na ke da tabbataccen bege, Tun Yesu ya zo wurina. Wata rana zan zauna tare da shi can, Tun Yesu ya zo wurina. KORUS 3) Ɗanuwa, kana so ka yi murna kuma? Bar Yesu ya cece ka yau. Za ya gafarta maka duk zunubanka. Bar Yesu ya cece ka yau. KORUS NA ƘARSHE Bar Yesu ya cece ka yau, Bar Yesu ya cece ka yau, Za ka yi kwanciyar rai, Har da murna sosai, In Yesu ya cece ka yau.Съна Бени Oh, Dios eterno, tu misericordia Kim sana güç veriyor Lal leh Hukdampa يا مراية Худо фиристод Писараш Исоро ความรักมั่นคง Oslavuj, Pána oslavuj mạ ạ̉ḥly ạlsjwd Я песню пою
Song not available - connect to internet to try again?