1) Alhamdu ga Allah don Ɗansa, Yesu. Ya ba da jininsa domin fansarmu, Amma dai ya tashi, ya koma Sammai. Ya kan ba da Ruhu, da yawan kyautai. KORUS Madalla! Madlla! bari kowa ya ji. Madalla! Madalla! dukan kowa ya bi. Ku zo wurin Allah ta wurin Yesu, Yi masa godiya don Mai Cetonmu. 2) Ya ceto cikakke, kyautar Allahnmu! Kowane mai tuba, mai ba da gaskiya, Kowane mai laifi, kome laifinsa, In ya zo gun Yesu zai sami gafara. Korus 3) Mu kuwa waƙar yabo ce mu ke ta yi. Ga Allah don Ɗansa, shi ne masoyi. Amma za mu ƙara yin murna sarai, Sa'ad da muka gan shi da ido sosai. Korus如今我把你们交托神 Иноят 'Ku Cari Suatu Panji Il tuo nome ليه بنخاف ليه Lodarti per la tua grandezza Shattan 2016 trek 01 (mınýs) mn yqym sạknaⁿạ La gå og la Gud Co to za nie zliczony tłum
Song not available - connect to internet to try again?