1) Allah Maɗaukaki, Sarki madauwami, Mu yabe ka. Kai ne Mahalicci, kai ne mai aminci, Kai ne mafifici har abada. 2) Mun taru wurinka, kai ne madogara, Mun yabe ka. Kai ne mai ƙaunarmu, kai ne mai fansarmu, Kai ne mai tsaronmu har abada. 3) Bayyana girmanka, nuna darajarka, Kusance mu. Tsarkake zukata, sauko da ikonka, Furta maganarka, ya Allahnmu. 4) Mallaki ƴaƴanka, ƙarfafa bayinka A duniyan nan. Yi amfani da mu, kwaƃi ragwancinmu, Mai da mu nan gaba manzanninka.Dieu règne en juste Roi Бог велел Ною построить ковчег ขอความรัก ขอฤทธา 众百姓清早到耶稣那里 Jesteś radością mojego życia 得胜在乎耶和华 Он знает ạlmsyḥ qạm неден яврум юзгюн дурдун ۇلۇۇ قۇداي! كۅز چاپتىرسام االامعا
Song not available - connect to internet to try again?