1) Allah ya kira shugaba Na duk mala'ikun sama Ya ce "Zan aike ka a duniya" Ya ce "Na yarda Ubangiji" "Ga ni, ka aike ni ko yanzu." 2) "Ka sabka, ka je duniya" Za ka iske budurwa, Sunnanta Maryamu ne." Mala'ika ya bar gaban Allah, Mala'ika ya bar gaban Allah, Ya zo, ya iske Maryamu. 3)Ya ce, "Allah ya aiko ni Da saƙonsa mafi tsarki Shi ne Yesu Ruhunlahi, Shi za ya shiga mahaifarki, Shi za ya shiga mahaifarki Shi ne 'Allah tare da mu". 4) Buduruwa ta razana Ta ce, "Ni buduruwa ce Ban taɓa shafe namiji ba". Mala'ika ya ce, "Gaskiyarki," Mala'ika ya ce, "Gaskiyarki," "Ba ki taɓa shafi miji ba". 5) "Ai, wannan ikon Allah ne, Ni ma, na ji tsoro ƙwarai. Da ni da ke, duka ɗaya ne. Mu bar wannan ga Ubangiji, Mu bar wannan ga Ubangiji," In ji Mal'ika Jibra'ilu. 6) Buduruwa ta ɗauki ciki Ta wurin Ruhun Mai Tsarki Ta haifi Macecin ƴan Adam, Shi ne Yesu Almasihu, Shi ne Yesu Almasihu, Shi za ya shirya duniyan nan.بنلاقيك وسط المصاعب Сүйүүсүн Себүүчү + Pouring Your Love O, o, cerul e în inima mea Ветер жизни Padáme na svoju tvár Ember, ne félj a rossztól Nunca Me Deixou Tárd ki a szíved Мəним үчүн гызылдан да баһа E dincolo de cer senin
Song not available - connect to internet to try again?