1) Almasihu, hasken duniya, Begen dukan masu rai, Yesu Rasul, Kalmar Allah, Tun fiI azal kai kaɗai. [Kai kaɗai madauwami ne, Kai kaɗai maɗaukaki.] 2x 2) Kai ka ajiye rigar mulki, Ka bar duk don cetonmu. Zafin mutuwa ba ka ƙi ba, Duk ka sha don ƙaunarmu. [Karƃi yabo, karƃi mulki, Naka ne har abada.] 2x 3) Mutuwa ta rasa iko Bisanka, Mai Nasara. Lahira ta buɗe ƙofa, Ka shiga, har ka fita. [An ɗauke ka can a Sama, Aikinka ka gama nan.] 2x 4) Duk jama'a suna jiran Zuwanka, ya Almasihu, Duk Ekklesiya tana zarnan Kewarka, Mai Cetonta. [Zo da sauri, muna bege, Zo, mu dinga ganinka.] 2x 5) Al'ummai, ku kasa kunne, Shi ne Ubangijinku. Ruhun Allah, jawo mutane Zuwa sawun Mai Cetonsu, [Ɗan Maryamu, Tsatson Dawuda, Ibnu Llahi, Ɗan Mutum.] 2xТахтънда Отурана Ве Кузу'я Seasons Йюджелтеджеим Исмини fy ạlạwl kẖlqtny̱ Náš Pán prebýva na chválach A Jesucristo quiero llegarme Shadow of Your Wings tạ̉ml 3 Миладын Сəбəбкары El Shaddai, El Shaddai
Song not available - connect to internet to try again?