1) Almasihu, pa babba, kai ne dutsen cetonmu. Sa mu cikin inuwarka, bar mu shiga kariyarka. Duk mun kasa adalci, duk mun aika zunubi, Kai madogararmu ne, kai dai matserarmu ne. 2) Ko mun kawo sadaka, ko mun daina ratsewa, Dukan namu ƙoƙari ba ya iya cetonmu. Kai kaɗai matsakanci, aikin sulhu naka ne. Mutuwarka da tashinka su sun kawo gafara. 3) Ga mu nan gun giciyenka, muna jiran ikonka. Kau da dukan zunubi, rashin ƙwazon Masu Bi. Da jini mai daraja, wanke mana zukata. Tsarkake mu duk yanzu don mu cika nufinka. 4) Ya maƃuyar tsarkaka, nuna ƙarfin cetonka. Ba mu ikon nasara, tsai da ikon magauta, Kwaƃi duk muguntarsu, rushe duk dabarbaru. Sai ka taya mu yanzu, ƙarfafa rayukanmu.Не оставляй меня мой Бог Дорогое имя Иисуса Svoje túžby vzdám Ближе к Тебе gǔ lǎo de qióng cāng Ómir jolynda jigermen júremiz Sukacita Hatiku Церковь Божия ты невеста у Христа mwsyqy̱ Боже, бляс'кът Ти изпълня
Song not available - connect to internet to try again?