1) Almasihu yana nan! Tsoron mutuwa ya ƙare. Wannan muka gaskata, Ikon kabari banza ne. Halleluya! 2) Almasihu yana nan! Ƙofar rai shi ne ya buɗe. Mutuwa fa ƙaura ce Zuwa rai na har abada. Halleluya! 3) Almasihu yana nan! Dominmu ne shi ya mutu. Tsarkin zuciya wajib ne Ga waɗanda ya fanshe su. Halleluya! 4) Almasihu yana nan! Ba mai hana mu ƙaunarsa. Ko da rai ko babu shi, Mun sa kanmu a hannunsa. Halleluya! 5) Almasihu yana nan! Mai sarautar dukan duniya. Sai mu bi ta gurbinsa, Mu yi mulki cikin Sama. Halleluya!Gdym ja pod krzyżem gdzie Jezus zmarł أفرح بيك On hyvä veisata Xudovandga yangi bir qoʻshiq ayting Gebed КЪМ ТЕБ МЕ ПРИБЛИЖИ Deň ku koncu sa chýli Превыше всех Živý je Pán في اسم يسوع نصرنا أكيد
Song not available - connect to internet to try again?