1) Ba da labarin mutuwar Yesu, Jini ya bayar domin cetonmu, Amma ya tashi, ya ci nasara, Ceto za a samu wurinsa kaɗai. KORUS Ba su labari, ba su labari, Yawancinsu ba su ji ba. Masu zunubi su tuba su bi shi, Yesu Mai Cetonsu ne. 2) Ba da labari ga mazaje duk, Ba za su tsira ba, sai dai sun ji. Ba da labari a wurin mata, Don su ma su tuba su ba da gaskiya. Korus 3) Ba da labari don yara su ji, Su ƙanƙanana su gane su bi. Ko masu yawa, ko ɗaya kaɗai, Mu ba su labari da ƙwazo sosai. Korus 4) Ba da labari ga duk mutane, Ko sun ji daɗi, ko wasu sun ƙi. Yi ta addu'a da bangaskiya, Maganarsa tana da iko sosai. KorusСен Гючлю Танръсън Давно давно ты утомлен Die tyd is hier İsa, Seni Seviyorum dm ạlrb ạsẖtrạnạ Vďaku Bohu vzdajme wǒ men shǒu lā zhe shǒu Ты воскрес المعمدان شفيعنا АЗ ЩЕ ПЕЯ НОВА ПЕСЕН
Song not available - connect to internet to try again?