Babban mai magani 'na nan, Yesu mai jin tausayinmu. Mu je mu nemi warkewa A wurin Almasihu. KORUS Yesu! suna mai dadin ji, Ba mai kamarsa, ba mai fi. Ina sonsa kamar me! Yesu Almasihu. Mai ba da lafiya ne shi, Cuta fa zunubanmu. Mu je mu roki gafara A wurin Almasihu. Mai kawo gafara ne shi, Ya dauke zunubanmu, Ya kai su bisa itacen A cikin jiki nasa. Nan gaba za mu yabe shi, Mun komo lafiyayyu. Ba magani na zunubi Sai wurin Almasihu. Amma da dangi masu yawa Da ba su da cetonsa, Mu sai mu je mu neme su, Mu kai su wurin Yesu.Nikdo z nás hodinu nezná Seigneur, du sein de la poussière Abandonne ta vie Имя Господне - крепкая Башня Bak, Ellerini Sana Uzatıyor Раб Иса'да зафер вар Әйса мениң Қутқазғучим Кайсы жол менен барам? Инде күп еллар үтте Рахмет Саган Аке
Song not available - connect to internet to try again?