1) Babban mai magani 'na nan, Yesu mai jin tausayinmu. Mu je mu nemi warkewa A wurin Almasihu. KORUS Yesu! suna mai daɗin ji, Ba mai kamarsa, ba mai fi. Ina sonsa kamar me ! Yesu Almasihu. 2) Mai ba da lafiya ne shi, Cuta fa zunubanmu. Mu je mu roƙi gafara A wurin Almasihu. Korus 3) Mai kawo gafara ne shi, Ya ɗauke zunubanmu, Ya kai su bisa itacen A cikin jiki nasa. Korus 4) Nan gaba za mu yabe shi, Mun komo lafiyayyu. Ba magani na zunubi Sai wurin Almasihu. Korus 5) Amma da dangi masu yawa Da ba su da cetonsa, Mu sai mu je mu neme su, Mu kai su wurin Yesu. KorusНебеса поют песнь Агнца To Know Your Name Bolaligimizdan sharaf aytamiz Опять зашумели народы zhǔ a wǒ suàn shén me Bol smutný som a sám Бардыгын кармап туруучу Azi Domnul este Jésus est mon divin Berger Sogno
Song not available - connect to internet to try again?