1) Dā can, da Sama ta cika da yabo, Nan kuwa zunubi ya ƙaru sosai, Yesu ya fito, ya shigo nan duniya, Abin godiya,--Jagorana ne. KORUS Kauna ta sa shi ya mutu domina, Hukuncina ya kau da shi duk Ya baratad da ni, gama ya tashi. Yana fa zuwa--ranar daraja. 2) Da aka kai shi kan dutsen Kabari, Har aka kashe shi kan giciye. Ya sha wahala, da raini da zagi Domin zunubanmu, Mai Fansata. Korus 3) Da aka binne shi can cikin kogo, Aikin ya ƙare, yanzu hutawa. Mala'iku suka lura da wurin, Begen ƴan Adam, Mai Cetona ne. Korus 4) Kabari fa ba ya iya riƙonsa, Ƙofa ta buɗe, Yesu ba ya nan, Ya ci nasara a kan mutuwa kuwa, Yana can Sama, Ubangijina. Korus 5) Sai wata rana, ƙaho zai yi ƙara, Za a ga ɗaukakar Yesu sosai, Tare da tsarkaka, Yesu zai dawo, Zan ɗaukaka shi, Yesu nawa ne. Korusإنى أحب الرب KHUAKIP AH TUANBIA CHIM AWK KAN NGEI sạybyn ṭrqnạ ەل۔شادداي Gdy się Chrystus rodzi 主为我们 Келе көр, Ыйса, мага Fiam, egyetlen kincsem vagy Их Эзэнийг магтъя Este é un povo
Song not available - connect to internet to try again?