1) Dā ina zaune cikin duhuna, A cikin bautar zunubai. Ban sani Yesu yana sona ba, Ban kula da cetonsa ba. KORUS Amma Allah ya ƙaunace mu, Ya ba da Ɗansa domin ya mutu, Don kada mu ma mu mutu Amma dai mu sami rai. 2) Shaiɗan ya ɗaure mini zuciyata A cikin halin hanyarsa. Ya hana mini hasken gaskiya Ya hana ni in bi Yesu. Korus 3) An kawo mana wa'azin ceto, An kawo mana gaskiya, Yesu ya kawar mini duhuna, Ya sa ni cikin hanyarsa. Korus 4) Yanzu jin daɗi kullum na ke yi, A cikin hanyar gaskiya. Na sami ceto daga zunubi, Rai na har abada. Korus 5) Sai wata rana Yesu za ya zo, Ya ɗauki dukan Masu Bi. Ni ma zan tafi can tare da shi, In zauna fa a gabansa. Korusالحرب الروحية - جزء ثان За грешных нас 主是全地的审判者 كەلىڭدەر سابيگە، ادال جۇرەكپەن bạrfḍ wbạ̹ṣrạr KA HNGAK THIUTHEO من ألفين سنة fy jbl qdsy أروح بحملي لمين Ya Yesu, Ban da Kai, Ban Iya Kome Ba
Song not available - connect to internet to try again?