1) Da cuta da gajiya a jeji can na ke, Sai Yesu ya same ni, ya rungume ni fa. Ya sa ni cikin garkensa da farinciki mai yawa. KORUS Ƙauna ta neme ni, jini ya saye ni, Jinƙai marar iyaka ne fa! Jinƙan Yesu, ba misalinsa! 2) Miyagun zunubaina ya wanke mini duk. Ya kori tsoron raina ya ba ni ƙaunarsa, Ya ce da ni ni nasa ne, ba wanda za ya raba mu. Korus 3) Azabar da ta samo gafarar laifina, Jininsa da ya wanke ƙazantar zuciyata, Ina misalin raɗaɗi wanda ya sha saboda ni! Korus 4) Yanzu a nan gabansa a cikin haskensa, Gun Yesu na ke zaune, Yesu Mai Cetona. A ƙare dukan yabonsa? Ko rabi ba na iyawa. Korus 5) Gabansa na ke zaune da daɗin rai yanzu. Zuwansa na ke jira domin ya kira ni. A Sama can in tarbe shi wanda ya zo ya cece ni. Korusۅزۉن ىيساعا ارناپ قويعون Hudaýy gözläň يا رب وحد lw tzwl ạlsmạ الرب قد ملك لبس الجلال Ga Yesu Ubangijinmu, Can Yana Mutuwa Время Я нуждаюсь в Тебе Иисус Wielki dzień nadchodzi
Song not available - connect to internet to try again?