1) Da duniyan nan da girmanta da yawan daɗin rai Su dā sun jarabce ni, sun kama ni sosai. Amma da dukan daɗinsu ban ƙoshi ba daɗai, Gama raina ba ya ƙoshi in ban da kai kaɗai. Yesu, Yesu, Yesu Gurasar Rai, Ban yarda ba, ban yarda ba a raba ni da kai. 2) Ko raina ya matsu fa, ko kewa na ke ji, Ko ina shan wahala, ko ciwo na ke yi, Ni sai in nemi Yesu, shi ne ya ce in zo, In faɗa masa duka, in roƙi taimako. Yesu, Yesu, Yesu Mai Taimako, Ban yarda ba, ban yarda ba a raba ni da kai. 3) Alkawarin Mai Cetonmu ba za ya tashi ba. Mai zuwa ba a ƙinsa in ya zo da gaskiya. Ina dalilin zafin zuciya, babu hutawa? Ga Yesu yana jira, ba iyakar tausayi. Yesu, Yesu, Yesu mai ƙaunata, Ban yarda ba, ban yarda ba a raba ni da kai.Tayyormisan Шел Христос пронзёнными ногами Perdon أملك فينا Ry Jesosy Tompo tsara Сендан Бошқаси Йўқ لو كان اسمك زي مسيحي ạ̹nsạn ạ̉yạ ạ̹nsạn Қадимда Худо Не унывай когда тернист твой путь
Song not available - connect to internet to try again?