1) Da yamman nan, ya Yesunmu, Albarkaci maganarka, Haskaka, Yesu, duhunmu Bishe mu kuwa da Ruhunka. Ya Yesunmu, mai taimako, Ƙarfafa ranmu duka yau. Ya Yesunmu, mai taimako, Ƙarfafa ranmu duka yau. 2) Magaucinmu ya bi mu yau. Da wayonsa, ya ruɗe mu. Jaraba ma mai zafi ce, Halinmu kuwa rarrauna ne. Ya Yesunmu, mai nasara, Ka cika mu da Ruhunka. Ya Yesunmu, mai nasara, Ka cika mu da Ruhunka. 3) Laifofinmu dayawa ne, Tunaninmu miyagu ne, Harshenmu duk da gurinmu, Sun ƙara mana laifinmu. Ya Yesunmu, yafe mu dai, Da jininka, ka wanke mu . Ya Yesunmu, yafe mu dai, Da jininka, ka wanke mu. 4) Ya Ubangiji, Allahnmu, Ka tsare mu da daren nan, Da hannunka ka riƙe mu, Da ikonka, ƙarfafa mu. Ya Yesunmu, ka keƃe mu, Har safiya, ka tsare mu. Ya Yesunmu, ka keƃe mu, Har safiya, ka tsare mu.On Our Side Он Воскрес Воистину ทรงเปลี่ยนความเศร้าโศก Danza Как ты велик ʿạyzyn yạ rb Неизменна любовь Твоя ОСАННА Weselić się będzie Рəбб Гүдрəтли Шаһдыр
Song not available - connect to internet to try again?