1)Duba, Yesu yana zuwa. Dā ya mutu dominmu, Dubban dubbai, tsarkakansa, Duka za su rako shi. Halleluya! Halleluya! Za ya nuna ikonsa. 2) Duk jama'a za ta gan shi, Su da suka soke shi, Cikin tsoro za su san shi, Ba sa so su tarbe shi. Suna kuka, suna kuka, Suna duban Sarkinsu. 3) Dā ya zo da kalmar ceto, Dā ya zo da gafara. Za ya komo mai shari'a, Za mu taru gabansa. Wa zai tsaya, wa zai tsaya Cikin ranar fushinsa? 4) Shi da kansa za ya sauko, Ranar fansarmu ta zo, Za mu tarbe shi a hanya, Masu rai da matattu. Cikin Sama, cikin Sama Za mu ga Ubangiji. 5) Zo da sauri, Almasihu, Masu Bi 'na jiranka. Ƙarfii mulki, ƙarfi yabo, Naka ne har abada. Halleluya! Halleluya ! Zo da sauri, zo yanzu.Единственный Особенный Любимый ḥlm ḍạʿ Seni izdeım Кат волна птичка 亲爱的朋友 Multă vreme eu am rătăcit نقطة من دم يسوع Иса махаббатым Сен 千种辛万种苦 Бак, Тахтта Отуран Раб'бе
Song not available - connect to internet to try again?