1) Dukan sarautar duniyan nan, Da ikonta da girmanta, Game da kai, Mai Cetona, Ba na maishe su kome fa. 2) Ƴanuwana da abokaina Ba su da hanyar taimako, Amma a bisa giciye Yesu ya gama fansata. 3) I, jinin Yesu ne kaɗai Wanda ya shafe laifina, Mai yawan ƙauna hakanan, Ba waninsa a duniyan nan. 4) Haƙuri, ƙauna, taimako, Koyarwa, iko, gafara, Zuciya mai tuba, ceto duk, Shi Yesu ne mai bayarwa. 5) Ya Yesu Ubangijina, Nan gaba bawanka na ke. Zuciyata, raina, ƙaunata, Na ba ka duka, naka ne.يا ماشي وعارف لوين للرب الأرض وملؤها mạtfkrsẖ ktyr dh yswʿ wsṭ ạltʿb Большого призвания нет у меня Sevgim Soğumasın Инсанлар, сөјлəјин Duysun daalar, duysun taşlar Պատերազմը տվել ենք Քեզ Свет пролился
Song not available - connect to internet to try again?