1) Dā, ban san labarin Yesu ba, Cikin duhu na bi hanyata, Ban ko kula akwai ceto ba Gun giciye. KORUS Jinƙai marar iyaka ne fa. Gafara a yalwace ya yi, Har ya kau da dukan zunubi Kan giciye. 2) Da na ji labarin cetonsa, Na ji nauyin kayan laifina. Sai na tashi neman gafara Gun giciye. Korus 3) Duba yawan girman ƙaunarsa, Duba irin aikin gafara! Da jininsa ne ya fanshe mu Kan giciye. Korus 4) Daga nan na zama bawansa, Ya yarda ya zama Sarkina. Akwai murna cikin zuciyata Don giciye. KorusЯ люблю Тебя Боже люблю всей душой موسيقي - زي النسر لما أرى الدم S novým nadšením Ya Rəbbin أنا هو الرب الشافي Sen Davosan Exodus xv Eleviamo lodi al Signore Doamne Tu-n necazuri lângă noi rămâi
Song not available - connect to internet to try again?