1) Dā can, da Sama ta cika da yabo, Nan kuwa zunubi ya ƙaru sosai, Yesu ya fito, ya shigo nan duniya, Abin godiya,--Jagorana ne. KORUS Kauna ta sa shi ya mutu domina, Hukuncina ya kau da shi duk Ya baratad da ni, gama ya tashi. Yana fa zuwa--ranar daraja. 2) Da aka kai shi kan dutsen Kabari, Har aka kashe shi kan giciye. Ya sha wahala, da raini da zagi Domin zunubanmu, Mai Fansata. Korus 3) Da aka binne shi can cikin kogo, Aikin ya ƙare, yanzu hutawa. Mala'iku suka lura da wurin, Begen ƴan Adam, Mai Cetona ne. Korus 4) Kabari fa ba ya iya riƙonsa, Ƙofa ta buɗe, Yesu ba ya nan, Ya ci nasara a kan mutuwa kuwa, Yana can Sama, Ubangijina. Korus 5) Sai wata rana, ƙaho zai yi ƙara, Za a ga ɗaukakar Yesu sosai, Tare da tsarkaka, Yesu zai dawo, Zan ɗaukaka shi, Yesu nawa ne. Korusโอ พระวิญญาณ เราเรียกร้อง Holy Spirit Thou Art Welcome У мен билан مەسىھ ئەيسا قۇدرەتلىك Panie, otwórz usta moje EC-NS Kako je predivno ime to (What a Beautiful Name) Ей Танръмъз, ей Кралъмъз فرحا أفرح بالرب Исо билан бирга юр сен Голгофа есть место греха и позора Ey Allah'ım Ey Allah'ım
Song not available - connect to internet to try again?