1) Dā ina zaune cikin duhuna, A cikin bautar zunubai. Ban sani Yesu yana sona ba, Ban kula da cetonsa ba. KORUS Amma Allah ya ƙaunace mu, Ya ba da Ɗansa domin ya mutu, Don kada mu ma mu mutu Amma dai mu sami rai. 2) Shaiɗan ya ɗaure mini zuciyata A cikin halin hanyarsa. Ya hana mini hasken gaskiya Ya hana ni in bi Yesu. Korus 3) An kawo mana wa'azin ceto, An kawo mana gaskiya, Yesu ya kawar mini duhuna, Ya sa ni cikin hanyarsa. Korus 4) Yanzu jin daɗi kullum na ke yi, A cikin hanyar gaskiya. Na sami ceto daga zunubi, Rai na har abada. Korus 5) Sai wata rana Yesu za ya zo, Ya ɗauki dukan Masu Bi. Ni ma zan tafi can tare da shi, In zauna fa a gabansa. KorusGel Allah, sor bana Rabbim beni tanıyor الرب يهوه إلهي Mi dedico a te Втікають дні ЯСА МУСА'ЙЛА ВЕРИЛДИ Dziatkom przyjść O suflete ce eşti iubit şi-ales งามเลิศประเสริฐ Magnificent Verím, lebo dal si mi vieru
Song not available - connect to internet to try again?