1) Dā, na zauna cikin zunubi, Ba na kula da Ubangiji, Ko mutuwa wadda shi ya yi Kan giciye. KORUS Jinƙan Yesu, ba misalinsa, Ya yi mini aikin gafara. Kayan laifina ya ɗauka kuwa Kan giciye. 2) Na ji zancen ladan zunubi. Tsoron mutuwa ya kama ni. Sai na roƙi jinƙan Mai Ceto Kan giciye. Korus 3) Na yi murna marar iyaka Tun da Yesu ya yi cetona. Ina rera waƙar yabonsa, Ba fasawa. 4) Nufina in kawo daraja Wurin Yesu Ubangijina, Sa'an nan in dubi fuskarsa Har abada.ครองราชย์องค์พระเยซู Reign King Jesus reign Бог ще те носи Rab Yücedir, Övgüye Layıktır Saisis ma main craintive مرني أن آتي إليك Apri il tuo cuor Ta parole لو كانت عيني Мой Отец возьми на Своё крыло V temne vzplála hviezda nám
Song not available - connect to internet to try again?