1) Ga ƙofa nan, buɗaɗɗiya, Mai Ceto ne ya buɗe. Dukan mai so ya sami rai Ya bi ta wannan ƙofa. KORUS Ga ƙofa dai buɗaɗɗiya Mai Cetonmu ya buɗe ta. Ku zo, mu je, Ku zo ku shiga dai. 2) Ga ƙofa nan a buɗe dai Kowa ya iya shiga Mawadaci da talaka Na kowace kabila. Korus 3) Ku matso zuwa ƙofan nan, Yanzu ne loton jinƙai. Ku karƃi rawani na rai. Kyauta ce wannan duka. Korus 4) Mai Cetonmu ya mutu dai Domin ƴan Adam duka. Ya buɗe ƙofar samun rai, Dukan mai so zai samu. KorusOh my Lord Keď mesiac svieti krásne Каждый мой день Тобой наполнен Seigneur, dirige et sanctifie ناس كتير على اسمك కన్నీటి బాధను విడుచుచున్న Acı Bana Ya RAB Trăit-am ani din viaţa mea Жүрегімді өзгерт, о Құдай Ием Если бы не Ты
Song not available - connect to internet to try again?