1) Ga taro can mai girma kuwa, har ba mai ƙirgawa, Al'ummai, dangi, harshe duk, kowane iri kuwa, Suna tsaye gun Allahnsu, yafe da adalci, Ga shaida kuwa ta nasara a cikin hannunsu. 2) Sun ta da murya kuwa sun ce, ceto ga Allahnmu, Yabo ya hau ga Allahnmu, duk da Mai Cetonmu. Mala'iku da dattawa sun haɗa bakinsu, Sun fāɗi bisa fuskarsu loton sujadarsu. 3) Albarka, girma, godiya, ga Allah, suka ce, Wadata, iko, ceto kuwa, har dukan zamanai. Yafaffun nan, ka shaida su? Daga ina su ke? Rigunan nan da suka sa, don me walƙiyarsu? 4) Domin maganar shaidarsu, tun suna duniya, An kashe su don suka ƙi su yi musun Yesu. I, domin shaida ga su nan, ba shakka, ba tsoro. Hidimar Allah za su yi dare. da rana kuwa. 5) Yunwa ba za su ƙara ji ko ƙishi ba daɗai. Rana ba za ta buga su a gidan Allah ba. Ɗan Allah ne mai kiwonsu, shi fa zai bi da su. Hawaye daga idanu, Allah zai share su.دالاما كوز سالسام، وتكەندى ويعا السام Ta Parole est la richesse Yesu Ubangijinmu Ne, Shi Ne Sarkinmu Севгин ичимде ท่านอยากจะพ้นจากความบาปของท่านหรื Would You be Free from the Burden of Sin Invoque-moi et je te répondrai Lord, Who at Cana's Wedding Feast ప్రేమసాగరా! ఈ ధరమరణ مش هاخاف Çox günahlar etmişəm, çoxların incitmişəm
Song not available - connect to internet to try again?