1) Halleluya! Halleluya! Halleluya! Wahalarka, Mai Fansarmu, Ta kawo ceto dominmu, Ta buɗe rijiyar rai yanzu, Halleluya! 2) Aikin Shaiɗan da gurinsa, Ka ƃata su da giciyenka, Ka ba da rai domin mu rayu, Halleluya! 3) Kai ne kaɗai mai nasara Kan Shaiɗan duk da ƴaƴansa, Ka kā da su da ikonka, Halleluya! 4) Kai ne ka jawo mu wurinka, Kai ne ka kawo gafara, Kai ne ka ba mu Ruhunka, Halleluya! 5) Kai ne ka gama cetonmu, Ka hau can Sama dominmu, Kai ne mai zuwa dominmu, Halleluya! 6) Yabo ga Allah sai mu yi, Yabo ga Yesu, Masu Bi, Yabo ga Ruhu Mai Tsarki, Halleluya!Alma mía no delires Roi de majesté بإيمان ورجاء Pokój po bojach, światło po ćmach A kegyelem árad Głowa, ramiona إلقاء 2 И до краев земли ạ̉skb rwḥk ʿlynạ Inn i festlig hall
Song not available - connect to internet to try again?