Halleluya, Halleluya, Halleluya. 1)Ya Yesu, muna yabonka, Mun taru don mu girmama ka, Mu yi sujada gabanka. Halleluya! 2) Ya Kalmar Allah, Shaidarsa, Bayani ne na darajarsa, Haskaka mu har abada. Halleluya! 3) Ka gyarta mini zuciyata Ka sa yabo a bakina, Domin in yi ta ɗaukaka ka. Halleluya ! 4) Ban da kai, raina wofi ne, Aikina kuma banza ne, Daɗi sai wurinka kaɗai. Halleluya! 5) Annabi, manzo, malami, Mai ta' aziyya, adili, Yabo gare ka mu ke yi. Halleluya! 6) Yaushe zan duba fuskarka? Yaushe ma zan ji muryarka? Sai ran da ka karƃe ni can. Halleluya!Kutsal, Kutsal, Kutsal Rab Such an Awesome God Kom nära Mig Basym we tizara Kisazo Un Gingtute Haw تەڭىر كەلدى تۉنكۉسۉن باققا /4 Sláva Bohu naveky في ليلة من الشتاء 主我尊祟你 Для меня нет преград
Song not available - connect to internet to try again?