1) Halleluya mu raira ma Ubangiji sabuwar waƙa. Mu raira Yabonsa cikin taron jama'arsa. Bari Isra'ila ya yi murna cikin wanda ya yi shi. Ƴan Sihiyona su yi murna cikin tsarkinsa. KORUS Mu yabi sunansa sa rawa. Mu yabi sunansa da murna. Raira yabai gareshi Da tambarin duma da giraya. 2) Gama Ubangiji ya kan ji daɗin mutanensa. Za ya sa masu tawali'u jamali da ceto. Bari tsarkakansa su yi kirari cikin ɗaukaka. Su yi rairawa don farin ciki bisa shimfiɗarsu. Korus 3) Maɗaukakin yabai na Allah kasance baƙinmu. Takobi kuma mai kaifi biyu cikin hannuwanmu. Domin a hukunta sakaya bisa al'umai. Horo kuma mai tsanani a bisa mutane. Korus 4) An ɗaure sarakunansu da manyan sarkoki. An ɗaure hakimansu da maruruwa na ƙarfe. An hukunta masu shari'a wadda aka hukunta. Wannan daraja ta dukan tsarkakansa ce. KorusInvoco Te Почему ты стоишь в стороне Нуждаюсь я в Тебе Nech vrchy odstúpia It's Rising Up Господь - моя твердиня моя башта Praise Him, Praise Him, Praise Him in the morning yạ fạdy ạlạ̹nsạn gẖny Если ты любишь
Song not available - connect to internet to try again?