1) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Kai Sarkin Isra'ila, shafaffen Allahnmu, Cikin sunan Maɗaukaki, ka zo ka cece mu. 2) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Mutanen da sun ɗiba gazarin dabino, Sun shimfiɗa a hanyarka domin ka taka su. 3) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Yau dukan jama'arka sun kawo yabonsu, Domin su gai da sarkinsu wanda ya fanshe su. 4) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Ka shiga Birnin Ƙudus, ya kai mai nasara, Tawali'u da yardar rai sun kai ka mutuwa. 5) Hosanna ga Ɗan Dawuda1 Mai albarka ne shi Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Loton da ka ke duniya, wahala ce ka sha, A hannun daman Allah, aka ba ka ɗaukaka. 6) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Ya Yesu Almasihu, Allah Maɗaukaki, Kai ne Mai Ceton duniya, ya kai Mai Tsarki.Uitstap: Hosanna shì jiè shàng suī yǒu hěn duō de kǔ nán Кәлдим бүгүн مەن سيىنۋشىمىن Láska Kristova je tak nádherná 主啊你是我一家之主 Yesu Ne, Yesu Ne, Shi Ya Panshe Ni ạ̹dyny ḥạjẗ ạ̉ʿysẖ lhạ ạ̉sẖkrk rby ʿly̱ ạlywm dh Господь со мной сомненьям места нет
Song not available - connect to internet to try again?