1) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Kai Sarkin Isra'ila, shafaffen Allahnmu, Cikin sunan Maɗaukaki, ka zo ka cece mu. 2) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Mutanen da sun ɗiba gazarin dabino, Sun shimfiɗa a hanyarka domin ka taka su. 3) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Yau dukan jama'arka sun kawo yabonsu, Domin su gai da sarkinsu wanda ya fanshe su. 4) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Ka shiga Birnin Ƙudus, ya kai mai nasara, Tawali'u da yardar rai sun kai ka mutuwa. 5) Hosanna ga Ɗan Dawuda1 Mai albarka ne shi Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Loton da ka ke duniya, wahala ce ka sha, A hannun daman Allah, aka ba ka ɗaukaka. 6) Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Ya Yesu Almasihu, Allah Maɗaukaki, Kai ne Mai Ceton duniya, ya kai Mai Tsarki.찬양 받으시기 합당하신 Бұл Өмірде อยู่เพื่อพระองค์ผู้เดียว I Simply Live For You Распускаются почки душистые Я твій Бог Hak Etmedik Jézus, megígérted وساننا، وساننا yạ ʿdrạ ṣwrtk Кел, Құдайға тағзым етуге
Song not available - connect to internet to try again?