1) Ina misalan daraja da ban mamaki da Jamalinka ya bayyana, ya Allah, haskena! 2) Ya Allahna Madauwami, kwarjininka ya sa In yi maka sujada fa a cikin zuciyata. 3) In ƙaunace ka kullum kuwa, mai iko duka ne, Don ka yarda ka zo guna, ka nemi ƙaunata. 4) Ba wani uba na duniya, ba wata uwa kuwa, Da za su iya renonmu yadda ka ke mana. 5) Sai abu ɗaya na ke so, in zauna gabanka, In ga jamalin haskenka, in dinga sujada. 6) In yi shelar sunanka dai, in riƙa tunani Yadda ka ƙaunace ni kuwa, ya Allah mai jinƙai. 7) Ina misalin daraja da ban mamaki kuwa Na tsarin dukan hikima wadda ka ayana.Amagire Dawıllarda ترد المسلوب На твоем и моем столе Не бросишь меня Иисус я люблю Тебя Asla bırakmazsın Moʻjiza boʻldi 2 В скорбный час я взываю к Тебе Siempre te alabaré
Song not available - connect to internet to try again?