1) Ina son Mai Ceto, Yesu, Ƙaunarsa ce zancena, Ina murna domin giciyen, Can ya kau da laifina. KORUS Ina waƙar Almasihu, Jininsa ne fansata, Tashinsa ne shaidar ceto, Babu sauran la'ana. 2) Ina cikin bautar Shaiɗan, Yesu ya ji tausayina, Sai ya zo ya ba da ransa, Yesu, ba mai kamarka. Korus 3) Ina ɗaukaka sunansa, Ƙarfin mutuwa ya ci, Har ya sa in yi tarayya Cikin nasara da shi. Korus 4) Ko a can a gunsa zaune, Ko a duniya saukakke, Kauna ce ta haɗa ranmu, Ni da Yesu ɗaya ne. KorusSevgi Boʻlsin Oramizda Sevgim Olmasa Seceraţi întruna Рожден حبيبي Я прихожу к Тебе Господь Iza moa io Zazakely قۇتقاردىڭ كۇنا قۇرساۋىنان نسجد لك Luodut, te Herraa kiittäkää
Song not available - connect to internet to try again?