1) Isowar Yesu a duniyan nan Al'ummai za su ji tsoro. Za su ce ma duwatsu da fannu, Ɓoye mu daga fuskarsa KORUS Wannan ƙarshen ranar Allah ce. Wanene za ya tsaya a ranan nan, m'm, Ko kun tuba da toka a ranan nan, m'm, Za a ce babu dama . 2) Za ya ce, "Na aiko Yesu Kiristi". Ku kun ƙi ku karƃe shi. Kun giciye shi a bisa itace, Domin ba ku ƙaunarsa. Korus 3) Ni ma ranar ramawata ta zo. Zan saka ma kowa. Bisa gwalgwadon aikin da ya yi Da kuma ladansa. Korus 4) Ranan nan ba cewa, "Ya Allahmu, Kai ka zalunce mu", Shi kuma za ya ce, "A'a mutane, Ni ban zalunce ku ba ". Korus 5) Za ku ce "Mun tubu, ya Allahmu" Shi za ya ce, "ba dama". Za ku ce, "ka yafe mu, ya Allah". Za ya ce, "babu dama". Korus 6) Za ye ce "Jinin Yesu na ba da shi, Domin zunubanku." Wannan ya isa domin fansarku Ku kun ƙi bangaskiya. » Korus 7) Na gama, na gama, kun shiga wuta nan. Da na shirya ma Shaiɗan. Wayyo ! Allah mun shiga azaba. Ku kun shiga ba tausayi. KorusFiglio prodigo Avec ton Esprit Každý deň mwḍwʿ ạ̉bthạjnạ Under His Wings ¿Qué Me Puede Da Perdón? Le peuple qui marchait أحببت أن سيدي Блажен народ у которого Господь есть Бог Ҳаётам дар Ту
Song not available - connect to internet to try again?