1) Ka haƙura, ya raina, haƙura. Ubangiji kuwa yana wajenka, Ka haƙura, kome dai ya same ka, Azaba, sakewa, ko damuwa. Ga Allahnka zai shirya mafakatka, A ƙarƙashin fukafukansa kuwa. 2) Ka haƙura, ya rai na, haƙura. Sa'ad da taimako ya katse ma, Loton da abokai suka yashe ka, Babu dalili na yin fargaba. Ka dogara ga Allahnka kaɗai, Zai ƙarfafa zuciyarka sosai. 3) Ka haƙura, ya raina, haƙura. Masifa, mutuwa, ba ƙarshenmu ba. Ka tuna, ƴanuwanka duka fa, A hannun Yesu mai nasara ne. Da mu da su ma fita duhun nan, Ma shiga hasken Allahnmu a can. 4) Ka haƙura, ya raina, haƙura. Haƙuri maganin duniya ne. Talauci ne ko rashin lafiya, Ko damuwa ko kuwa hargitsi ne, A cikin Ruhun Allah ga murna, A cikin ƙaunar Yesu, ta'aziyya.ىيسام مەنىن، سەن جۅنۉندۅ ىرىم Da Yesu Za Mu Kwana علمني أنتظرك يارب wǒ men zài qī dài Sevinç Mahabbatyńnyń bir ushqyny meniń, jan-dúnıeme tıdi Bly volhard soos atlete Бог е казал Сравнится ль кто с Творцом Da Suna Wanda Ba Mai Fi A Dukan Zamanai
Song not available - connect to internet to try again?