1) Ka haƙura, ya raina, haƙura. Ubangiji kuwa yana wajenka, Ka haƙura, kome dai ya same ka, Azaba, sakewa, ko damuwa. Ga Allahnka zai shirya mafakatka, A ƙarƙashin fukafukansa kuwa. 2) Ka haƙura, ya rai na, haƙura. Sa'ad da taimako ya katse ma, Loton da abokai suka yashe ka, Babu dalili na yin fargaba. Ka dogara ga Allahnka kaɗai, Zai ƙarfafa zuciyarka sosai. 3) Ka haƙura, ya raina, haƙura. Masifa, mutuwa, ba ƙarshenmu ba. Ka tuna, ƴanuwanka duka fa, A hannun Yesu mai nasara ne. Da mu da su ma fita duhun nan, Ma shiga hasken Allahnmu a can. 4) Ka haƙura, ya raina, haƙura. Haƙuri maganin duniya ne. Talauci ne ko rashin lafiya, Ko damuwa ko kuwa hargitsi ne, A cikin Ruhun Allah ga murna, A cikin ƙaunar Yesu, ta'aziyya.Ҷаҳонро бо чунин ҳусну тароват Nezomriem 영광의 왕 찬양합니다 sẖwf bʿynk Мы превозносим Тебя YERİNİ ALDIN Паруса надежды Allahnmu Garu Mai Ƙarfi Если яркий день померкнет и исчезнет солнца свет الراعي الأمين
Song not available - connect to internet to try again?