1) Kamar ruwa ya kan sauko Bisa duniya busasshiya, Haka Ruhun Ubangiji Cikin can Ekklesiya, Sauko nan, ya Ruhun Allah, Sauko, muna kishinka. (2x) 2) Kamar raƃa ta kan faɗo Bisa ƙasa, ta kan tsaya, Ba ta fita, sai ta gama Nata aikin warkarwa. Sauko nan, ya Ruhun Allah, Sauko, muna jiranka. (2x) 3) Kamar wuta ta kan cinye Dauɗa, cuta, ruƃewa, Haka Ruhun Ubangiji, Zauna cikin zuciya. Kau da ƙarya, dukan lafi, Kone su da wutarka. (2x) 4) Aikin Ruhu mu ke roƙo, Ƴaƴansa na lafiya. Ƙaunar Ruhu mu ke nema, Ƙauna marar ƙarewa, Ba mu su, ya Ruhun Allah, Ba mu su, ba fasawa. (2x)爱和原谅 Môj duch ťa túži chváliť ạlfjr sẖq wlạḥ Różyczka cudna wzrosła Per il mio amico Obediente A Tu Mandato mydly - lbldy bạṣly Qoning meni tozalar Pokój w Jezusie أطلقني حرًا
Song not available - connect to internet to try again?