1) Ko kun zo gun Yesu domin gafara? Yana kiranmu duka mu zo. Shi ya ba da ransa domin dukanmu, Sai ku zo wurin Yesu, ku zo. KORUS Sai ku zo, sai ku zo, Wurin Yesu Mai Ceto, ku zo. Shi zai tsarkake ku daga zunubi, Sai ku zo wurin Yesu, ku zo. 2) Kome yawan laifi fa zai wanke ku, Sai ku zo wurin Yesu tun yanzu. Za ku sami murna kuwa da kwanciyar rai, Sai ku zo wurin Yesu, ku zo. Korus 3) Almasihu Yesu yana jiranmu. Cikin gidan Ubansa ya hau, Yana shirya wuri don ya karƃe mu, Sai ku zo wurin Yesu, ku zo. KorusHoden si vzít Насиҳат sạ̉gẖny byn ạlnạs تأمل 6 'Take Up Thy Cross', the Savior Said Вся земля Господа славит إلتفتوا إلي واخلصوا Düşmüşdüm mən günaha,çox gəzdim qaranlıqda Il frutto dello Spirito Как мне быть без общенья
Song not available - connect to internet to try again?