1) Ku masu Ƙaunar Yesu fa, jama'ar Masu Bi, Ku kasance da halin da ya zauna cikinsa. 2) Ko cikin surar Allah, shi, girmansu ɗaya ne, Ya ƙanƙantad da kansa, har ya zama bawa, shi 3) Ya zama gurbinmu a nan, ya yi biyayya, shi, Biyayya har ga mutuwa, mutuwar giciye. 4) I, domin wannan Allah kuwa ya ƙara girmansa, Ya ba shi suna mafi kyau a bisa kowanne. 5) I, domin girman sunan nan, sunansa mafi kyau, Gwiwoyin dukan masu rai duk za su rusuna. 6) Kowane harshe cikinsu zai yi shaidar Yesu, Cewa shi Ubangiji ne don girman Allahnmu.Таурат, Забур, Інжіл мен Жазбадағы Anak-Anak, Pujilah Jak para život rozplýva sa wéi zhǔ shì qīn rén ربي جئت من أجلي Одаренные спасеньем 以琳赞 Exaltate Вот снова год прошел и грустно мне مادمت في سفيتني
Song not available - connect to internet to try again?