1) Ku mutanen Almasihu, Rera waƙa, dukanku. Sai ku faɗa wa jama'a Duk labarin cetonku. Albishir ne, Maryamu Ta haife shi, Ɗan Mutum, Sai fa godiya ga Allah Domin duk alherinsa. 2) Sa'an nan ya ƙara girma. Cike da tagomashi, Shi Ɗan Allah yana koya Mana hanyar adalci. Idan mu amintattu ne, Idan mun bi sawunsa, Za ya kai mu wurin Uba, Za mu sadu wurinsa. 3) Wajibi ne sai mu bi shi, Domin yawan ƙaunarsa. Shi ya sha wahalar giciye, Ba don ya yi laifi ba. Laifofin jama'a duka Suka kai shi mutuwa. Ƙofar rai ce shi ya buɗe Don ya kai mu fadarsa, 4) Sai in yi masa sujada, Allahna da Sarkina. Sai in bauta masa kullum Da iyakar ƙarfina. Sai da dukan hankalina, Sai da dukan zuciyata, Zan bi Yesu, Mai Cetona, Cikin ikon Ruhunsa.Rinascere La mattina lodo il Signore NEM TEIN AN AUH عايز أتمتع بيك يسوع أغلى من اللآلىء Илгээлтийн дуу Has aumentado Doux Agneau sans tache Духом наполняй
Song not available - connect to internet to try again?