1) Ku ta da zuciyarku, kada ta ƃaci kuwa, Ƴanuwan ba su mutu ba, su barci su ke yi. An shirya zamansu a gidan Sama can, Allahnmu ne ya kira su su fita duniyan nan. 2) Ba sauran zunubi, jaraba ba ta can, Wahala duk da ƃacin rai ba za su shiga ba. Su, Yesu su ke bi da muryar nasara, Sunansa yana goshinsu, sun duba fuskarsa. 3) Mun ajiye jikinsu can cikin kabari Har ran da za a ta da su marasa ruƃewa. Shi Yesu Fansarmu, shi ne mai ba da rai, A cikin rashin ruƃa dai, shi za ya ta da su. 4) Mun gode, Allahnmu, domin bangaskiyarsu, Don shaidarsu a wurinmu, kwatancin halinka. Ya Ubangijinmu, ka ƙarfafa mu yau Domin mu bi sawunsu har mu gama aikinmu.凡事都不可亏欠人 تمر السنين غني Králi slávy velebený Nebo sa sklonilo k zemi Venid y Adoremos Spirit move mn wyn yyjy لا يغفو ولا ينام mzmwr 139
Song not available - connect to internet to try again?