1) Ku zo mutane duk Ku furta laifofinku yau A gaban Yesu Mai Ceto, Shi zai yi gafara . 2) Idan da zafin kishi yau Cikin masu bin Yesu. Ba za su yi albarka ba Idan da kishin nan. 3) Ƴanuwa, ku bar kishi Ku bar ƙeta, ku bar ƙarya Ku bar zina, ku bar gulma Ku bi Mai Cetonmu. 4) Idan da waɗannan abu A cikin zukatanmu yau Me za mu ce ma Yesu Ran da mun kai sama? 5) Shi zai ce ku tashi nan Ku tashi nan, ku tashi nan Shi zai ce ku tashi nan Ni dai ban san ku ba. 6) A ranan nan sai kumya Kumya mar-iyaka Sai kuka mai zafi kuwa Da cizon haƙora. 7) Masu bi, mu yi anniya Domin ranar zuwansa Zai ce da mu bayin kirki Ku shiga murnarku. 8) Taimake mu, ya Yesu Ka bi da mu da Ruhunka Domin mu aika nufinka Har ran da za ka zo. 9) Halleluya ga Yesu Ga Yesu Mai Cetonmu. Halleluya ga Yesu, halleluya Amin Ga Yesu Mai Ceto.E prezent aici Fiul lui Dumnezeu فاجئتني Siempre Conmigo Esta Anhelo Trabajar Por El Señor Научи меня Господь смиряться Un giorno migliore Ma petite lumière Христос Спаситель Az Úrnak lelke rám száll a magasból ạ̹rfʿ ʿynyk lfwq
Song not available - connect to internet to try again?