1) Lokacin da ka ke shan wahala fa, Lokacin da Shaiɗan ya ke damunka, Tuna da alherin Ubangiji inka, Wannan dai zai ba ka karfin zuciya. KORUS Har matuka Yesu yana nan Har matuka Yesu yana nan Har matuka Yesu yana nan Shi ba zai rabu da kai ba, ko kaɗan. 2) Sa'ad da ka duba masu dukiya, Tuna da alkawarin Mai Cetonka, Rai madauwami ne shi ya ce zai bayar Ga duk wanda ya ke ba da gaskiya. Korus 3) Idan ka gaji da halin duniya, Kana neman rabuwa da ruɗinta, In ji Ubangiji, "Ina jiranka, Zo, ka karƃi hutawa a wurina." Korus 4) Ko a matse ka ke, babu fasawa, Shaiɗan yana neman ƃata halinka, Sai ka ta da murya ga Allahnmu, Shi ba za ya yarda ba ka lalace . KorusVon den Gipfeln der Welt Isten Báránya Pour quel péché, Jésus Pán Boh je Pastier môj После проливных дождей Տերն է իմ Արքաների Արքան بقربك يا حبيبي يسوع إليك يا يسوع أمين Così come sei
Song not available - connect to internet to try again?