1) Mai Ceto yana ƙaunata, Shi Makiyayina ne. Tun Yesu yana kiwona, Ni ba na rasa kome. KORUS "Ku zo gare ni, dukanku, Ku masu nauyin kaya, Ni ma in ba ku hutawa," In ji shi, Masoyina. 2) Dā ina zaman tayarwa, Na ƙi tafarkin Yesu, Sai ƙaunarsa ta jawa ni, Ta sa ni cikin garke. Korus 3) Nan gaba dai, Ubangiji Kullum zai bi da raina A cikin hanyar adalci Sabili da sunansa. Korus 4) Ko cikin kwarin mutuwa, Ba zan ji tsoro ba fa, Ba wanda za ya taƃa ni, Tun Yesu yana sona. Korus 5) Ƙaunarsa marar ƙarewa Nan gaba za ta bi ni. A cikin gidan Allah kuwa Har abada zan zauna. KorusКел балалар ән салайық Дертлерими ким билир? Садедже Иса hl ystṭyʿ ạlrb by Джесурун Езгиси يوم ما قابلتك Palabra fiel es de Jesús bsmʿ ạlạ̉dẖn Dosť, dosť už mám! Мадақтаймын, ән саламын Hay gozo en mi corazón
Song not available - connect to internet to try again?