1) Mai yin ƙarya, ka bar yin ƙaryarka. Ka zo, ka tuba, ki zo, mu tuba Domin mu bi Mai ceto Mai yin tsafi, ka bar yin tsafinka, ka zo, ka tuba. ki zo, mu tuba domin mu bi Mai-ceto. KORUS Ƴan'uwana, turbaya ne muka zo. Turƃaya ne za mu, tuƃaya ne za mu koma Mun zo cin kasuwa, turƃaya ne muka zo, Turƃaya ne za mu, turƃaya ne za mu koma. 2) Mai shan giya, ka bar shan giyanka ka zo, ka tuba. ki zo, ki tuba domin mu bi Mai ceto Mai shan taba ka bar shan tabanka. ka zo, ka tube, ki zo, ki tuba domin mu bi Mai ceto. Korus 3) Mai aure biyu, ka bar yin aure biyu, ka zo, ka tuba, ki zo, ki tuba domin mu bi Mai ceto Duniya nan akwai cuta cikinta. Akwai wahala, akwai azaba, duniya za ta shuɗe fa. Korus 4) Kana da mata, mai cin amanarka, Kada ka damu, akwai shari'a A ranar zuwan Yesu. Kina da miji, mai cin amanarki. Kada ki damu, akwai shari'a, a ranar zuwan Yesu. Korusحدثوني عن يسوع T'offrirò Plesaj, Božia rodina ВОДЕНИТЕ ОТ БОЖИЯ ДУХ Ich laufe zum Vater 教会要发光 گفتار مسيح Wznoszę ręce swe Я прошу Данъя данъя Кузё-Инмардэ тон
Song not available - connect to internet to try again?