1) Makiyaya da daddare sun tsare garkensu Mala'ikan Allah ya zo, ya haskaka su fa. 2) "Kada ku ji tsoro," ya ce, gama sun firgita, "Labarin murna ne na kawo ga dukan duniya". 3) "An haifi Almasihu yau, a birnin Dawuda fa, Mai Ceto, Ubangiji ne, alamarsa ke nan". 4) "Jariri za ku iske ma da siffar mutane A nannaɗe da tsummoki cikin sakarkari." 5) Da gama faɗin saƙon nan, taron haske ya zo, Mala'iku 'na rerawa, suna ta yin yabo. 6) "Ɗaukaka duk ga Allahnmu, salama ga duniya, Aminci ga mutane duk, yanzu da koyaushe."عايز اعيش Jesús Es Mi Rey Soberano 主为我们 Силерге каалап бакыт ạ̉wṣnạ Ven, es hora de adorarle Allah nə vəd etdisə Есүсийн нэр бүх газарт Szeretlek, Jézus ạ̹lqạʾ 9
Song not available - connect to internet to try again?