1) Mu bubbuɗe zukatanmu Ga Ubangiji Allah, Mu miƙa mar hadayarmu, Mu yi masa sujada Domin yalwar wadatarsa Da duk amfanin gona. Mun gode wa Ubangiji Domin kyautansa duka. 2) Mun girbe dukan gonaki, Ga dawa cikin rumbu. Mun tara dukan amfani Na aikin hannuwanmu. Wannan ne fa abincinmu Na rai a wannan duniya. Kullum fa ka ciyad da mu Da abinci na ruhu. 3) Mun yi wahalar damuna, Mun sha gajiya ainun, Amma a ƙarshen yini fa Ka ba mu damar hutu. Ka sa mu zama zaƃaƃƃu Na ƴaƴan fari naka, Mu cika aikinka a nan, Mu shiga hutu naka. 4) Ƙasar can mai albarka ce, Ƙasa ta mulkin Allah. Can dai akwai itacen rai, Da kuma kogin Allah. Duk tsarkaka sun taru can, Mu kuma za mu bi su, Mu yi ta yabon Allah can, Don ya albarkace mu.كتابي جميل Когда приходит рождество Afară ninge cu fulgi mari ارتفع على السماوات ḥty̱ mạ hdẖạ ạljfạ ليك كل الكرامة والمجد والسلطان مين زيك Ny lohan'ny eklesia dia Jesosy Tompony Keď otvorím Písmo, čítam v ňom Ziua Domnului soseşte Sionul se pregăteşte
Song not available - connect to internet to try again?